Wannan Course Din Zai Koyar Da Kai Yadda Zaka Fahimci Duniyar Digital Da Sirrinta, Daga Mataki Na Farko Har Zuwa Matakin Da Zaka Iya Amfani Da Wayarka Ko Laptop Naka Domin Neman Ilimi, Ayyuka, Da Damar Samun Kudi Kai Tsaye Daga Ko Ina.
Za Ka Fahimci Yadda Duniya Ta Canza Daga Analog Zuwa Digital, Abubuwan Da Ba Kowa Ya Taba FaÉ—a Maka Ba Game Da Intanet, Da Yadda Za Ka Yi Amfani Da Zubin Fasaha Don Gina Kanka A Zamanance
An Tsara Wannan Course Ne Cikin Harshen Hausa Kai Tsaye, Babu Kalamai Masu Nauyi Da Zasu Baka Wahalar Fahimta. Ko Kai Matashi Ne Da Bai San Komai Game Da Intanet Ba, Ko Mace Ce Dake Gida Da Ke Neman Ilimi Don Shiga Harkar Internet, Wannan Course Zai Bude Maka Idanu Ka Fahimci Abubuwan Da Zasu Canza Rayuwarka, In Sha Allahu.
 Me Za Ka Koya A Wannan Course Din?
-
Menene Digital World, Da Yadda Ta Sauya Rayuwarmu
-
Sirrin Amfani Da Wayarka Wajen Koyon Ilimi Da Nemawa Kai Mafita.
-
Yadda Ake Yin Amfani Da Internet Don Samun Ilimi Da Bayanai
-
Yadda Za Ka Kirkiri Accounts Da Amfani Da Google Drive, Docs, Words, Da Sheets
-
Yadda Ake Karatun A Makarantun Online Kamar Udemy, Coursera, Simas Academy, Malamiromba
-
Muhimmancin Tsare Sirri A Intanet Da Kare Kanka Daga Matsaloli
-
Yadda Zaka Yi Amfani Da WhatsApp Business, Zoom, Da Sauran Kayan Aiki
-
Canza Tunaninka Domin Amfani Da Intanet Ta Hanya Mai Kyau
-
Gano Scammers, Ponzi Schemes, Get Rich Quick Shemes Da Sauransu
-
Yadda Zaka Shirya Rayuwarka Ta Digital Don Gaba
 Wannan Course Din Zai Taimakawa:
-
Matasa Masu Sha’awar Ilimi Na Zamani Da Internet
-
Matan Gida Masu Sha’awar Shiga Harkar Internet
-
Dalibai Da Ke Da Wayar Hannu Ko Computer
-
Mutanen Da Suke So Su Canza Rayuwarsu Ta Hanyar Intanet
A Nan Ba Iya Digital Literacy Zaka Koya Ba, Wannan Shi Ne Tushen Ilimin Duniyar Intanet Gabadaya.









Reviews
There are no reviews yet.